Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon tare da Jim Yong Kim, shugaban bankin duniya za su ziyarci yankin manyan tabkuna na Afrika a wannan makon domin mika goyon bayan ganin an aiwatar da muhimmin shirin yarjejeniyar zaman lafiya, kamar yadda rahotannin suka nuna a jiya Litinin. Mataimakin kakakin majalissar Eduardo Del Buey wanda ya sanar da wannan lokacin taron manema labarai na duk rana ya ce, shugabannin biyu za su ziyarci kasashe 3 a wannan shiyya na Afrika, wato jamhuriyar demokradiya na Kongo, Ruwanda da kuma Uganda bayan babban magatakardar ya kammala ziyarar shi a kasar Mozimbique a gobe Laraba 22 ga wata.
Mr. Eduardo ya ce, makasudin wannan ziyara shi ne domin ba da goyon baya ga wannan yarjejeniya ta zaman lafiya da tsaro, da kuma fitar da wani tsari na hadin kai ma jamhuriyar demokradiya na Kongo da ma yankin baki daya.
Shi dai wannan tsarin kasashen Afrika 11 na da sauran kungiyoyin kasa da kasa guda 4 wanda aka ma lakabi da kasashe 11 da 4 suka rattaba hannu a kan sa da farko a birnin Addis Ababa na kasar Habasha a ranar 24 ga watan Fabrairu. Ita dai wannan yarjejeniya, an yi ta ne da zumar kawo karshen tashin hankalin da ake yi a kasar Kongo da kuma na gabashin kasar na Kongo har ila yau, sannan kuma a shimfida zaman lafiya mai dorewa a yankin da ya dade yana fuskantar rikici.
Mr. Ban kuma zai isa birnin Addis Ababa bayan kammala wadannan ziyara na yankin manyan tabkuna na Afrika, domin halartar babban taron cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar tarayyar kasashen Afrika OAU da yanzu ta koma AU, inda zai yi ganawa ta musamman a kan tsaro, zaman lafiya da hadin kai da za'a nuna ma jamhuriyar demokradiya ta Kongo da ma yankin baki daya, in ji Eduardo del Buey.(Fatimah)