Shugaban kasar Amurka Barack Obama da matarsa Michelle za su fara wani rangadin aiki na mako daya a kasar Senegal, Afrika ta Kudu da Tanzaniya a karshen watan Yuni, a cewar fadar White House.
Shugaba Obama, a yayin wannan ziyara a nahiyar Afrika daga ranar 26 ga watan Yuni zuwa ranar 7 ga watan Yuli, na fatan karfafa da bunkasa huldar tsakanin Amurka da wadannan kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, musammun ma wajen karfafa bunkasuwar tattalin arziki, demokaradiyya, zuba jari da kasuwanci, da kuma mai da hankali kan shugabannin Afrika na zamani mai zuwa, in ji kakakin fadar White House, mista Jay Carney.
Obama zai gana da shugabannin wadannan kasashe, shugabannin kamfanonin kasuwanci da shugabannin kungiyoyin zaman kansu a yayin wannan ziyara ta farko da zai kai a nahiyar Afrika tun bayan wa'adinsa na biyu.
Wannan ziyara kuma za ta jaddada niyyar shugaban kasar Amurka wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin Amurka da kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara domin bunkasa zaman lafiya da cigaba a wannan shiyya, in ji mista Carney. (Maman Ada)