in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin bunkasa na Afirka ya sanya bunkasuwar Afirka kan 4.8 a shekarar 2013
2013-05-29 10:09:19 cri

Bankin bunkasa na Afirka AFDB cikin hasashe da ya yi na saurin bunkasar tattalin arziki a nahiyar a shekarar 2013 na nuna cewa, saurin bunkasar zai kai kashi 4.8 cikin dari, kana a shekarar 2014, zai haura zuwa 5.3, bisa la'akari da albarkatu dake kara yawa a nahiyar.

A cikin kundin hasashen da bankin ya yi na bana wanda aka wallafa ranar Talata, an ce, samun saurin bunkasar zai dogara ne kan yin gyara, ta yadda za'a sauya yanayin amfana daga albarkatun ta hanyar samar da ayyuka, yin amfani da kudade da ake samu wajen haraji yadda ya kamata da kuma taimakawa masu zuba jari da jama'a su yi hadin gwiwa.

Rahoton na cewa, albarkatun noma, ma'adinai da makamashi za su iya kawo bunkasar tattalin arziki da kuma bude hanyar bunkasuwar jama'a.

Bankin bunkasa na Afirka ya ba da rahoton ne bayan da tsohon darekta janar na hukumar cinikayya ta duniya, Pascal Lamy ya bayyana Afirka a matsayin sabuwar jagorar ci gaba a karni na 21, inda ya yi kira ga nahiyar ta shawo kan wasu kalubale dake gabanta don ta samu cimma burinta.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China