Shugaba Xi ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci yankin Lushan da bala'in ya fi shafa, inda ya bukaci kananan hukumomi da su kimanta irin barnar da bala'in ya haddasa, kana su tsara wani shirin farfadowa a matakin kananan hukumomi.
Xi ya ce kamata ya yi shirin ya yi la'akari da tattalin arziki da yanayin yankin, tare da samar da dama ga yankunan da bala'in ya shafa ta yadda za a farfado tare da samun ci gaba.
Ya ce kamata ya yi gwamnatocin yankunan su fito da tsare-tsaren farfadowa da suka dace wadanda za su kai ga zuba jari, kudin shiga, cin gajiyar filaye, samar da aikin yi da kuma tsaron jama'a.
Idan ba a manta ba a ranar 20 ga watan Afrilu ne wata girgizar kasa mai karfin mako 7.0 ta abkawa yankin Lushan, inda mutane a kalla 196 suka mutu. (Ibrahim)