in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shugabannin kungiyar AU karo na 21
2013-05-27 16:02:42 cri

A ranar 26 ga wata, an kaddamar da taron shugabannin kungiyar AU karo na 21 da za a shafe kwanaki 2 ana yinsa a birnin Addis Abba, hedkwatar kasar Habasha, shugabanni, da kusoshin gwamnatoci, da wakilai na mambobin kasashen kungiyar AU sama da 50 tare da sakataren janar na M.D.D Ban ki-moon da kuma shugabar kwamitin kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma sun halarci taron.

Taron da aka yi na wannan karo ya sha bamban da irin na wadanda suka gudana a baya, a wannan rana, ba a shirya bikin bude taron ba, amma a maimakon haka, an yi taron koli na kungiyar AU cikin siri kai tsaye, kuma kungiyar AU ba ta fayyace hujjar yin hakan ba.

Taken taro na wannan karo ya yi daidai da na karon da ya gabata, wato "Dunkulewar kasashen Afrika baki daya da farfado da nahiyar", inda aka tattauna batun dunkelewar tattalin arziki na kasashen Afrika baki daya, da halin tsaro da ake ciki, da shirin raya nahiyar cikin shekaru 50 masu zuwa. Bayan da aka kammala taron koli da aka yi cikin siri a wannan rana da safe, shugabannin kasashe mambobin kungiyar AU 13 da sakatare janar na M.D.D. Ban ki-moon da shugabar kwamitin kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma, da shugaban karba-karba na kwamitin AU na wannan karo Haile Mariam da sauran shugabannin kasashen Afrika, sun halarci taron manema labaru, inda aka bayyana matakan da aka dauka wajen yaki da cututtuka a kasashen Afrika, musamman ma wajen yaki da cutar sankarau da cutar tarin fuka, da ta zazzabin cizon sauro da ke addabar nahiyar.

A yayin taron manema labaru, Ban ki-moon ya nuna yabo game da nasarorin da kasashen Afrika suka samu a wannan fanni, kuma ya kara da cewa, M.D.D. za ta ci gaba da goyon baya game da wannan, yana mai cewa, "Tun daga shekarar 2001, yawan mutanen da suka kamu da cutar sankarau a nahiyar ya ragu da kashi 1 cikin 4, haka kuma, yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar zazzabin cizon sauro ya ragu da kashi 1 cikin 3. Nasarorin da aka samu a nahiyar Afrika ya danganta da kokari na ko wace kasa a nahiyar Afrika. M.D.D. za ta ci gaba da yin hadin gwiwa kafada da kafada da nahiyar, sabo da tana ganin cewa, batun kiwon lafiya yana da muhimmanci sosai wajen raya nahiyar. "

Kullum batun tsaro babbar matsala ce da ke cima nahiyar Afrika tuwo a kwarya wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma, sabo da haka, dukkan tarurrukan koli na kungiyar AU da aka yi a baya, su kan mai da hankali sosai a kan wannan matsala. Duk da kyautatuwar halin tsaro da aka samu a nahiyar, a karkashin shugabancin kungiyar AU, musamman bayan da aka kafa kwamitin kula da batun zaman lafiya da karko na kungiyar a shekarar 2004, amma ya zuwa yanzu, akwai sauran rina a kaba game da wannan batu.

A cikin shekarar da ta gabata, an rasa daukar matakai masu inganci wajen warware rikici na kasashen Mali da Afrika ta tsakiya, wani lokaci ma, har kuma ana bukatar kasashen waje don su ba da taimako wajen warware batun tsaro na kasashen Afrika, amma, wannan ya kan kawo sarkakkiya game da wadannan batutuwa. A gun wannan taron koli na kungiyar AU, shugabannin kasashen Afrika da dama sun cimma daidaito a tsakaninsu, wato ya kamata kasashen Afrika su warware batun tsaro nasu da kansu.

A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana da yamma, shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya fada wa wakilinmu cewa, matakan da kungiyar AU ta dauka game da batun kasar sun nuna cewa, kasashen Afrika na da karfi wajen daidaita batun tsaro na kansu, a cewarsa: "Bayan shekaru 22, a karkashin taimako daga kungiyar AU, kasar Somaliya ta sake zama mamba a kungiyar AU, kuma yanzu, sojojin kungiyar AU na gudanar da aikin samar da zaman lafiya a kasarmu, don taimakawa sojojin gwamnatin wajen yaki da kungiyar ta'addanci ta Al-shabab."

Haka kuma, a wannan rana da yamma, kungiyar AU ta shirya wani takaitaccen biki don jinjina ci gaban da masu harkokin kimiyya suka samu a nahiyar, shugabar kwamitin kungiyar AU Madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta jaddada muhimmanci aikin nazarin kimiyya da kasashen Afrika suka yi, ta ce, "kungiyar AU tana ganin cewa, dole ne kasashen Afrika su gudanar da aikin nazarin kimiyya da ke da kalubale da ma'ana ta musamman sosai, domin sa kaimi ga raya tattalin arziki na nahiyar da kawo alheri ga jama'a."

Ban da wannan kuma, bikin murnar cika shekaru 50 da kafa kungiyar AU da aka shirya a yayin taron koli na kungiyar, shi ma ya jawo hankalin jama'a sosai.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China