An yi bikin cika shekaru 50 da kafa kungiyar AU
|
A ranar Asabar 25 ga wata, kungiyar kasashen Afirka (AU), wato kungiyar hada kan kasashen Afirka da aka kira a da (OAU), ta yi bikin cika shekaru 50 da kafuwarta a birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha, inda aka waiwayi tarihi da nasarar da ta samu, tare da yin shawarwari kan yadda za a kara bunkasa nahiyar Afirka mai albarka cikin lumana.
Baki daya kimanin mutane dubu 15 suka halarci wannan biki, ciki har da shugabanni da kuma tsoffin shugabannin kasashen duniya. Manzon musamman na shugaban kasar Sin, kana mataimakin firaministan kasar Sin, Wang Yang, da shugaban Faransa, Francois Hollande, da mataimakin shugaban kasar Indiya, Hamid Ansari, da sakataren harkokin waje na kasar Amurka sun halarci bikin.
A gun taron koli na AU kan tunawa da kafuwarta da aka yi a safiyar wannan rana, shugaban kungiyar a wannan karo, kuma firaministan kasar Habasha, Hailemariam Desaleg ya bayyana cewa, bikin zai hada kan mutane, domin kara sa kaimi ga bunkasa nahiyar Afirka yadda ya kamata. Ya ce,
"Yau wata muhimmiyar rana ce a tarihi, ba ma kawai ta nuna cewa wadanda ake nuna ma kiyayya da bambanci na launin fata sun sami babban ci gaba a fannin neman samun 'yanci da hadin kai ba, har ma ta nuna wani sabon mafari, wato kokari tare, da zummar cimma burin 'yantar da kasashen Afirka a fannonin siyasa da tattalin arziki."
A ranar 25 ga watan Mayu na shekarar 1963, shugabanni da kusoshi da kuma wakilan kasashen Afirka masu 'yancin kai 31 sun rattaba hannu kan tsarin kungiyar OAU a birnin Addis Ababa, inda aka yanke shawarar kafa kungiyar, tare da tabbatar da wannan rana a matsayin ranar 'yantar da kasashen Afirka. Daga bisani, kasashen Afirka sun fara bayyana ra'ayinsu a harkokin duniya bisa jagorancin kungiyar OAU.
A shekarar 2002, kungiyar AU ta maye gurbin kungiyar OAU, tare da aniyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da sa kaimi ga yin kwaskwarima da gudanar da tsarin rage talauci, da sa kaimi ga bunkasa nahiyar Afirka baki daya. Yanzu kuma kasashen Afirka na kokarin cimma burinsu na farfadowa a karkashin jagorancinta. A gun bikin da aka yi a yammacin ranar, shugabar kwamitin kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta waiwayi tarihi na tsawon shekaru 50 da Afirka ta yi a karkashin jagorancin kungiyar, ta ce,
"Muna nuna girmamawa ga masu gwagwarmaya wajen yaki da nuna bambanci ga launin fata. Zamanin nahiyar Afirka yana zuwa. Bari mu yi amfani da wannan zarafi mu samar da makoma mai kyau!"
A cikin 'yan shekarun da suka wuce, tattalin arzikin Afirka na bunkasa cikin sauri. Wannan yana da alaka sosai da zurfafa hadin gwiwa da sauran kasashen duniya, musamman ma kasashe masu karfin tattalin arziki suka yi tsakaninsu da kasashen Afirka. Hailemariam Desaleg ya nuna godiyarsa ta musamman a gun taron, inda ya ce,
"Wasu aminanmu sun yi kokari sosai wajen bunkasa manyan kayayyaki masu amfanin jama'a na Afirka. Yanzu zan mika godiya a gare su, musamman ma kasar Sin, wadda ta ba da kudin agaji sosai a wannan fanni."(fatima)