'Yan sandan sun tabbatar da harin bayan da mazauna jihar Borno suka kai rahoto cewa 'yan bindiga sun kai farmaki a gidan yari da misalin karfe 7 na daren lokacin wurin, ranar Alhamis.
Ana kyautata zaton cewa wadanda suka kai harin su ne wadanda suka kai farmaki a tashar 'yan sanda dake Gwoza a kan iyakar kasar Najeriya da Kamaru kwanaki 10 da suka wuce inda suka kashe mutane 8 har da dan sanda daya.
Kafar ta tsaro ta ce 'yan kungiyar Boko Haram din sun kai farmaki a gidan yarin ne saboda akwai wasu daga cikin mamabobinsu da aka cafke yayin hare hare na baya da ma kan wasu laifuka wadanda suke kulle a gidan yarin Gwoza.
Gwoza karamin gari ne dake da nisan kilomita 134 a kudu maso gabashin garin Maiduguri inda a nan ne ake fama da 'yan kungiyar Boko Haram, kuma a lokuta da dama gwamnatin Najeriya ta sha kafawa da kuma daga dokar ta baci a yankin saboda hare hare. (Lami Ali)