Manzon na shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya samu ganawa da shugaban kasar Togo, Faure Gnassinbe.
Bisa neman wannan kujera ta babban darektan BIT, kasar Nijar za ta gabatar da dan takararta kuma tsohon faraminista Ibrahim Hassane Mayaki, wanda a halin yanzu yake rike da matsayin sakataren gudanarwa na kungiyar dake kula da aiwatar da tsarin NEPAD.
A cewar hukumomin kasar Nijar, kasar Togo tana da babban matsayi a cikin wannan harka bisa dalilin cewa mamba ce a halin yanzu a cikin kwamitin zartarwa na BIT.
Ministan shari'a na kasar Nijar, Marou Amadou ya nuna cewa BIT wata kungiya ce dake da babban matsayi dake maida hankali kan harkokin da suka shafi aiki da ma'aikata a duniya musammun ma a nahiyar Afrika.
Bisa wannan ne yake fatan kasarsa zata taki sa'a ganin cewa ba a taba samun wani dan Afrika da ya yi jagorantar wannan kungiya ba tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1919. (Maman Ada)