Ana shirin kafa wata hukumar kula da daidaita lamuran sadarwa a kasar Nijar
A ranar Laraba, 'yan majalasar dokoki a kasar jumhuriyar Nijar, sun amince da tsarin dokar da ke ba da damar kafa wata hukumar sadarwa ta kasa a hukunce ,wato CSC, hukumar gwamnati da nauyin sa ido kan lamuran sadarwa ya rataya ga wuyan ta.Kamar yadda ayoyin dake cikin dokar da ta ba da damar kafa CSC suka yi amana, CSC hukuma ce ta gwamnati mai zaman kanta da ba ta da wata halaka da siyasa, wacce kuma za ta kula da sa ido kan daidaita lamuran sadarwa. Ita dai wannan hukuma aikin da ya rataya ga wuyanta shi ne, tabbatar da yancin ayyukan sadarwa, da sa ido kan aiki da dokokin gudanar da watsa labarai, da daidaita yanayi yadda dukkan 'yan kasa za su samu damar fadi albarkacin bakin su , haka kuma da ba da dama ga kungiyoyi masu zaman kansu, da jam'iyyun siyasa wanjen yin magana a kafofin watsa labarai na gwamnati. Hukumar CSC ita ce ke da damar ba da yancin bude gidajen rediyo da na telabijin a cikin kasar.(Abdou Halilou).
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku