in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an hukumomi 2 na MDD za su kai ziyarar kwanaki biyu a Kasar Jamhuriyar Nijar
2012-02-15 10:37:21 cri
Babbar Jami'ar hukumar kula da lamuran jin kai na gaggawa ta MDD,Valerie Amos da Helen Clark jami'ar hukumar MDD mai kula da cigaba da bunkasa rayuwar al'umma, za su kai wata ziyara ta kwanaki biyu a kasar Nijar, kamar yadda ofishin MDD ya sanar a ranar Talata cewar kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua.

Amos da Clark za su ziyarci kasar Nijar, daga ranar 16 zuwa 17 ga wata Febrairu kamar yadda jami'in sadarwa na OCHA hukumar kula da harkokin jin kai ta MDD ya sanar.

Wadannan jami'ai,Clark da Amos za su gana da shugaban kasar Mahamadou Issoufou, faraminista Birji Rafini da kuma wasu jami'an gwamnatin kasar ta Nijar.Ban da haka, jami'an za su kai ziyara a yankin Tillaberi da ke kudu maso yammacin kasar domin su ganema idanunsu yanayin da jama'a ke ciki a game da matsalar karamcin kalaci da kuma irin taimakon gaggawa da ya kamata a kawo musu domin su tinkari wanan matsala . Jami'in sadarwar, ya sanar da cewa ,Clark da Amos za su gana da wakilan kungiyoyin agaji da masu hannu da shuni a kan wanan lamari.(Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China