A jawabinsa shugaba Xi na kasar Sin ya ce ziyarar da Netanyahu ke yi a kasar Sin ta nuna cewa, gwamnatin Isra'ila da shi kansa Netanyahu sun dora muhammnci kan dangantakar dake tsakanin Sin da Isra'ila, don haka shugaba Xi ya ce ita ma kasar Sin ta dora muhimmanci sosai ga dangantakar da ke tsakin kasashen biyu.
Shugaba Xi ya kara da cewa, yana fatan yin musayar ra'ayoyi da Netanyahu kan dangantakar da ke tsakanin sassan biyu da kuma sauran batutuwa da ke shafarsu.
A nasa bangare Mr Netanyahu ya ce ya yaba da gagarumin ci gaban da Sin ta samu cikin shekarun da suka gabata idan aka kwatanta da abin da ya ga a shekaru 15 da suka gabata.
Netanyahu ya ce yana saran ganin kasashen biyu sun kara karfafa dangantaka tsakaninsu ta yadda za su kara cimma nasarori. (Ibrahim Yaya)