A lokacin taron, ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ya nuna fatansa na ganin cewa, kungiyar EU ta soke shawarar hana jigilar makamai da ta daukar wa kasar Syria, don bai wa jam'iyyar adawar kasar makaman zamani, sakamakon bambancin karfin makamai da ke tsakanin sojojin gwamnatin kasar da bangaren adawar.
Sai dai ministan harkokin wajen kasar Jamus Guido Westerwelle bai amince da shawarar da Fabius ya bayar ba, yana ganin cewa, ya kamata kungiyar EU ta mai da hankali kan ayyukan farfado da yankunan da ke karkashin mulkin jam'iyyar adawar kasar Syria.
Haka zalika, babbar wakiliyar kungiyar EU mai lura da harkokin waje da tsaro Catherine Ashton ta nuna cewa, a halin yanzu, abin da jam'iyyar adawar kasar Syria ta fi bukata shi ne taimakon da za a samar masu a fannin muhimman kayayyakin more rayuwa.
Madam Ashton ta ce kamata ya yi, a kawar da takunkumin tattalin arziki, da sha'anin kudi da aka dora wa kasar Syria, don jam'iyyar adawa ta iya samun taimakon magunguna da ruwa mai tsabta da dai sauransu. Tana mai cewa, ba za a iya warware batun Syria kwata kwata ba sai dai bin hanyar siyasa. (Maryam)