Kungiyar Boko Haram a Nijeriya ta dauki alhakin hare-haren da aka kai a wasu kauyuka a Arewacin Nigeriya
Kungiyar nan masu tsattsauran ra'ayin addinin da suka yi suna a 'yan shekarun nan wajen kai munanan hare-hare a arewacin kasar Nijeriya da babban birnin tarayyar ta Abuja a yau talata 10 ga wata suka fitar da wata sanarwar daukar alhakin kai hare-haren da aka kashe mutane 90, cikinsu har da 'yan majalisar dokoki biyu na jiha da na dattawa a Jos dake jihar Filato, tsakiyar arewacin kasar a karshen makon da ya gabata.
Sanarwar ta kuma dau alwashin cigaba da kai hare hare, tana mai karyata labarin da mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkar tsaro Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, ya yi cewa, ya samu lambobin wayoyin shugabanninta don su samu yin sulhu a tsakaninsu da gwamnati.