Wani gungun sasantawa na kungiyar kasashen Musulmi na OCI kan kasar Mali ya gudanar da wani zaman taronsa a ranar Litinin a birnin Djeddah, inda ministan harkokin wajen kasar Mali, mista Tieman Hubert Coulibaly ya bukaci gamayyar kasa da kasa da su taimaka wajen karbe makamai da gungun kungiyoyin da za su halarci taron sasanta 'yan kasa a cikin yanayi da lokacin da gwamnatin wucin gadin kasar Mali ta tsai da, a cewar wata sanrawa mai tushe.
A birnin Djeddah, jami'in diplomasiyyar kasar Mali ya nuna yabo kan manufar da aka cimma game da daidaita rikicin kasarsa, tare da bayyana cewa, kasar Mali za ta yi abun gwaji a dukkan yankin Sahel, a cewar sanarwar ma'aikatar harkokin wajen kasar Mali.
A karshen wannan taro na Djeddah, mahalarta taron sun jaddada amincewarsu ga hadin kan kungiyar OCI, da 'yancin kai da cikakken yankin kasar Mali, tare da yin kira ga 'yan tawayen MNLA da su ajiye makamai domin shiga shawarwarin zaman lafiya bisa sharudan gwamnatin kasar Mali. (Maman Ada)