in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Direktan ofishin kula da harkokin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin Wang Yi ya gana da Hillary Clinton
2011-07-30 19:41:21 cri
A ranar 29 ga wata, a birnin Washington, direktan ofishin kula da harkokin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Wang Yi ya gana da sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Hillary Clinton, kuma ya yi musayar ra'ayi tare da zaunannen mataimakin sakataren harkokin waje na kasar Walliam Burns game da batun Taiwan.

A yayin ganawar, bangarorin biyu sun bayyana cewa, mu'amala da aka yi tsakaninsu na da amfani sosai, ga kasashen Sin da Amurka wajen kara samun fahimtar juna game da batun Taiwan.

Wang Yi ya yi wa kasar Amurka bayani game da ra'ayin kasar Sin kan yanayin da ake ciki a yankin Taiwan da manufar da take aiwatarwa game da wannan yanki, kana yana fatan Amurka za ta ci gaba da cika alkawarin da ta dauka game da wannan batu, don nuna goyon baya ga raya dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan da samun bunkasuwa cikin lumana, don taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman karko a yankin Taiwan. Haka, Wang Yi ya sake jaddada matsayin da Sin take don nuna adawa ga yadda Amurka kan sayar da makamai ga yankin Taiwan.

Haka kuma, manyan jami'an Amurka sun yaba wa irin ci gaban dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan, kuma sun bayyana cewa, Amurka za ta ci gaba da nuna amincewa ga manufar kasar Sin daya tak a duk duniya. Haka kuma, Amurka tana fatan yanayin da ake ciki a yankin Taiwan zai ci gaba da samun kyautatuwa karko, kuma wannan ya dace da moriyar kasashen Sin da Amurka.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China