in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 16 sun mutu sakamakon harin da sojojin sama na kasar Amurka suka kai a arewa maso yammacin kasar Pakistan.
2012-10-12 16:47:57 cri

Ranar 11 ga wata, kafofin yada labaru ta kasar Pakistan sun ba da labari cewa, a wannan rana, jiragen sama na yaki na kasar Amurka wadanda babu matuka sun kai hari a yankin kabilar Orazkai dake arewa maso yammacin kasar Pakistan, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 16 yayin da wasu suka raunana.

Wannan ya kasance hari na 33 da sojojin Amurka suka kaiwa kasar Pakistan ta wannan hanya. An ba da labari cewa, ya zuwa yanzu, hare-haren da Amurka ta kaiwa yankin arewa maso yammacin kasar ya haifar da asarar rayuka a kalla 200.

Ko da yake, kasar Pakistan ta yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai tana mai cewa, hakan ya karya ikon mallakar yankunan kasar Pakistan kuma ya sabawa dokar kasa da kasa, amma sojojin Amurka ba su daina kai hare-hare kan Pakistan ba. A ganin Amurka, kai hare-hare ta hanyar jiragen saman da babu matuka ya kasance mataki mafi kyau wajen dakile 'yan bindiga dadi dake kan iyakar kasashen Afghanistan da Pakistan. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China