A wannan rana da karfe 3 da minti 50 na yamma, an tada bom da aka dasa cikin mota a wata tashar bincike ta sojoji masu tsaron iyakar kasa na rundunar soja da ba na cikakku ba ta kasar Pakistan dake girke a jihar Quetta da Bacha Khan, hargitsin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 ciki har da wani sojan tsaron iyakar kasa, yayin da mutane 50 suka ji rauni.
A wannan rana da misali karfe 5 da mintoci 40 na yamma, aka tada bom a wani wurin ibada dake yankin Mingora na lardin Khyber Pakhtunkhwa dake arewa maso yammacin kasar. Wannan lamari ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 22 yayin da wasu 65 suka ji rauni.
A kuma daren ran 10 ga wata, aka tada jerin boma-boman a birnin Quetta dake kudu maso yammacin kasar, daya bayan daya cikin 'yan mintoci. 'Yan sandan birnin sun sanar da cewa, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 82 yayin da wasu 121 sun yi rauni. Asibitoci sun ba da labari cewa sakamako irin munanan rauni da wasu mutane suka samu, watakila za a samu karin adadin asarar rayuka.
An ce, kungiyar soji ta Lashkar-e-Jhangvi da gwamnatin kasar ta yi watsi da ita, ta sanar da daukar alhakin aiwatar da wannan hari na boma-bomai a jere.
Shugaban kasar Asif Ali Zardari da firaministan Raja Pervez Ashraf sun yi Allah wadai da wadannan hare-haren da aka kai, kuma Raja Pervez Ashraf ya umurni hukumomi da su ba da jiyya mai kyau ga wadanda suka yi rauni. (Amina)