Wata kafar watsa labarai a kasar Pakistan mai suna Geo ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Taliban da ke Pakistan ta harbe har lahira jami'an tsaro 21 da ta sace a wani shingen duba ababan hawa da ke yankin arewa maso yammacin Pakistan kwanaki da dama da suka gabata.
Rahoton ya ce, an samu gawawwakinsu ne a yankin Hassan Khel kusa da Peshawar, kuma dukkansu an harbe su har lahira.
Buga da kari rahoton ya ce, kungiyar Taliban da ke Pakistan ta dauki alhakin kashe jami'an tsaron 21 da ta sace.
A ranar Laraba da dare ne 'yan kungiyar Taliban kimanin 30 dauke da makamai suka kaddamar da wani hari a wasu tashoshin binciken ababan hawa biyu a kudancin Peshawar, inda suka kashe jami'an tsaro 2, guda ya raunanna, kana suka sace wasu 23.
Kafar watsa labaran ta ce, biyu daga cikin jami'an tsaron da aka sacen sun tsere daga hannun Taliban din.(Ibrahim)