Kakakin da take bayani ga manema labarai a wannan rana tace, cigaban tattalin arzikin Afrika ya yi ta samun cigaba na kashi 5 cikin dari a ko wace shekara cikin wannan karnin da ake ciki a dalilin kayayyakin taimako da kasar Sin ta bada da kuma zuba jari.
Rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana furucin mataimakin firaministan Zimbabwe Arthur Mutambara, inda ya ce lokaci yayi da Afrika za ta daina daukar gudummuwar da Sin ke bayarwa da sunan wata soyayya ce daga kasar, ganin yadda ita kanta da take nahiyar Asiya ta tashi daga matsayin wata kasa mai fama da talauci zuwa kasar da ta habaka ta fuskar tattalin arziki a duniya.
A game da haka Hua Chunying ta ce, dangantakar da Sin ta kulla da Afrika wani abu ne da ya kamata, tana mai bayanin cewa, bukatun da Sin take yi wa Afirka ya sa Afrika ta habaka daga rikicin tattalin arzikin duniya da ake fuskanta fiye da wassu kasashe.
Kuma a cewarta, hadin gwiwwa tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afrika ya zama cude-ni-in-cude-ka wato kowa na amfana da dan uwansa kuma yana inganta ne saboda aminci da kuma mutunta juna. Har ila yau jarin da Sin ta zuba a nahiyar ya kusa kimanin dalar Amurka biliyan 20 a karshen shekara ta 2012, ban da dalar biyan 3 da ta kara wancan adadin daga baya duk a cikin wannan shekara.(Fatimah)