in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin kan Sin da Afirka yana amfanan bangarorin 2, in ji babban jami'in kasar Sin
2013-03-18 20:18:47 cri
Shugaban kungiyar diplomasiyya ta jama'ar kasar Sin, kana tsohon ministan harkokin wajen kasar, Mista Li Zhaoxing, ya furta a Litinin 18 ga wata a nan birnin Beijing cewa, matakan da aka dauka a baya sun shaida cewa, hadin kan kasar Sin da kasashen Afirka yana amfanan bangarorin 2, wanda hakan yake taimakawa kokarin samun walwala da ci gaba a Sin da Afirka.

Mista Li ya fadi haka ne a wani taron dandali mai taken 'masana'antun kasar Sin dake nahiyar Afirka', inda ya yi bayanin cewa, nan da wassu'yan kwanaki, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyara a karon farko, inda zai yada zango a kasashe 3 dake nahiyar Afirka, lamarin da a ganinsa zai daukaka zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi.

Kimanin shekaru 10 da suka wuce, nahiyar Afirka ta samu wata karuwar tattalin arziki da ta kai kashi 5%. Idan ba'a manta ba, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya taba yin hasashen cewa, saurin karuwar tattalin arzikin nahiyar Afirka a shekarar 2013 zai wuce matsakaicin saurin karuwar da za a samu a kasashe masu tasowa a duniya. Don gane da haka, Mista Li ya yi tsokaci game da cewar, Nkosazana Dlamini-Zuma, shugaban kungiyar AU, wadda ta ziyarci kasar Sin a kwanakin baya, da ta yi cewar, bisa yanayin da ake ciki na fama da rikicin hada-hadar kudi a duniya, hadin gwiwa dake tsakanin bangarorin Sin da Afirka shi ne wani muhimmin dalilin da ya tabbatar da saurin karuwar tattalin arzikin Afirka.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China