A yayin ganawar, Li Yuanchao ya bayyana cewa, Sin ta dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Afirka ta Kudu, tana son yin kokari tare da kasar Afirka ta Kudu wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito da kuma kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a dukkan fannoni. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana son yin mu'amala tare da jam'iyyar kwaminis ta kasar Afirka ta Kudu a fannin fasahohin raya jam'iyyar, da inganta dangantakar dake tsakanin jam'iyyun biyu tare da dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare.
Mataimakin shugaban jam'iyyar kwaminis ta kasar Afirka ta Kudu Solly Mapaila wanda ya jagoranci tawagar jam'iyyarsa yana son kara yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin jam'iyyun biyu, da koyin fasahohi daga juna, da kuma sada zumunci a tsakanin jama'ar kasashen biyu. (Zainab)