A yayin da ya ke ganawa da manema labaru a wannan rana, Zoellick ya ce, bayan abkuwar matsalar kudi a duniya, kasashen da suka fi samun saurin karuwar tattalin arziki suna samun bunkasuwa yadda ya kamata, amma kasashe masu ci gaba suna fuskantar matsaloli da dama wajen sake farfado da tattalin arziki. Bayan haka kuma, Zoellick ya kalubalanci shugabannin kasashen Turai da su yi kokarin tinkarar rikicin bashi, a sa'i daya kuma ya nuna cewa, da kyar ake iya yin gyare-gyaren tattalin arziki sakamakon wasu matsalolin da ke faruwa a tsarin kudi na kungiyar EU.
Kan yanayin tattalin arziki da ake ciki a duniya, Zoellick ya nuna cewa, akwai bambanci a tsakanin yanayin tattalin arziki da ake ciki a yanzu da yadda ake a lokacin matsalar kudi, saboda haka, mai yiwuwa ne ba a samu matsalar kudi da ta abku a shekarar 2009 ba. (Bilkisu)