in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU tana da babban buri game da Afrika
2013-05-10 11:03:33 cri

Shugabar kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU Nkasozana Dlamini-Zuma a jiya Alhamis ta ce, tana da babban buri a kan Afrika, wani yanki mai haske da za'a amfana da shi.

Madam Dlamini-Zuma ta ce, tun lokacin da kungiyar take amfani da sunanta na da wato OAU, ya zuwa yanzu da ta koma AU a cikin shekaru 50, an samu cigaba sosai a nahiyar.

Da yake jawabi, shi ma game da wannan biki, shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya ce, a cikin shekaru 50 da kafuwar kungiyar hada kan kasashen Afrika, yanzu ana dab da kaddamar da wassu manyan cigaba da nahiyar ta samu na kokarinta na zama wata nahiya mai makomar alheri.

Afrika, in ji shi, ta shimfida wani dandalin samun wadata na ciyar da kai, kuma za ta iya amfani da abubuwan da take da su domin daukan nauyin bukatunta, sannan har ila yau, ta yi cinikin albarkatun da take da su da sauran kasashen duniya.

Sai dai kuma shugaba Zuma ya yi nuni da cewa, ba za'a iya samun wata cigaba a nahiyar ba, idan babu zaman lafiya, ya lura da cewa, rigingimun da ake fuskanta a nahiyar yana daya daga cikin abubuwan dake kawo cikas a cigabanta.

Jacob Zuma ya kuma yaba ma kungiyar kasashen BRICS wadda kasarsa ke ciki, yana mai cewa, zama daya daga cikin mambobin kungiyar ya bai wa nahiyar wata dama na kulla alaka da sauran kasashen duniya.

A karkashin jigon "Isar da alkwari a kan Afrika", dandalin tattaunawar na tattalin arzikin da ake yi yanzu haka a kasar ta Afrika ta Kudu zai mai da hankali ne a kan abubuwa 3 da suka hada da yadda za'a iya rarraba tattalin arziki, inganta dabarun samar da ababen more rayuwa da kuma fito da hazakar da nahiyar ke da shi.

Daruruwan mutane ne daga kasashe fiye da 70 suke halartar taron WEF da za'a kammala shi a yau Jumm'a 10, agogon kasar.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China