Yayin taron tattaunawar da kwamitin harkokin wajen majalisar dokokin jama'ar kasar Faransa ya kira, Laurent Fabius ya bayyana cewa, cikin 'yan makonnin da suka gabata, kasashen Faransa, Amurka da kuma Rasha suna tattaunawa kan gabatar da wani jerin sunayen jami'an gwamnatin kasar ta Syria yanzu wadanda watakila ne jam'iyyar adawar kasar da kungiyar juyin mulkin kasar za su so yin shawarwari tare da su, don a warware matsalar Syria ta hanyar siyasa.
Laurent Fabius ya kara da cewa, shugaban kungiyar juyin mulkin kasa Mouaz Al-Khatib ya taba ambata maganar yin shawarwari tare da wasu jami'an gwamnatin kasar, amma ban da shugaban kasar Bashar al-Assad. (Maryam)