Ran 27 ga wata, yayin da ya ziyarci kasar Faransa, ya bayyana cewa, watakila ne kasar Amurka ta karfafa goyon bayan da take baiwa jam'iyyar adawar kasar Syria, ya kuma kara da cewa, kasashen Amurka, da Faransa suna kokarin neman hanyar gaggauta sauyin siyasa a kasar.
Bugu da kari, za a cigaba da tattaunawa kan batun yunkurin sauyin siyasa na kasar a taron 'abokan kasar Syria', wanda za a kira a birnin Rome na kasar Italiya ran 28 ga wata, inda ake sa ran jam'iyyar adawa ta kasar Syria, za ta shiga wannan taro don neman karin taimako, amma Kerry bai bayyana cewa, ko kasar ta Amurka za ta kara samar mata taimako ko a'a ba.
A wannan rana kuma, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Anatoly Bogdanov ya bayyana cewa, Rasha ta yi kira da a yi taro don warware matsalar Syira. Rasha za ta shirya wani taron tattaunawa tsakanin kasa da kasa ne a kasar don warware matsalar 'yan gudun hijira na kasar ta Syria. Amma yanzu, ba a tabbatar da lokacin kiran taron ba. (Maryam)