Bayan rangadin da ya kai a ofishin rajista ta hukumar 'yan gudun hijiran dake garin Tripoli a yankin arewacin tekun kasar Lebanon, Guterres ya ce rikicin na Syria na kawo tabarbarewar lamura a yankin da ma duniya baki daya don haka ya yi kira ga kasa da kasa su ba da karin taimako ga kasashen dake lura da 'yan gudun hijira.
Jami'in na MDD ya nanata godiya ga kasar Lebanon da jama'arta dangane da dimbin tallafi da suke baiwa 'yan gudun hijiran.
Hukumar 'yan gudun hijira ta MDD a cikin rahotonta na baya bayan nan ta ce yawan mutanen kasar Syria dake gudun hijira a kasar Lebanon ya kai dubu 336. (Lami Ali)