A yayin taron, Li Keqiang ya jaddada cewa, dole ne a dogaro da habaka bukatu a gida, tare da kyautata da kuma fadada kasuwanni a gida, a kokarin raya tattalin arzikin kasar Sin zuwa sabon mataki. Sa'an nan kuma ya zama tilas a mai da hankali kan raya tattalin arzikin kasar ta hanyar da ta dace kuma ba tare da tangarda ba. Har wa yau kuma wajibi ne a mara wa masana'antu baya wajen gaggauta kyautata tsare-tsarensu, da tabbatar da ganin aikin kirkire-kirkire ya kara taka rawa wajen bunkasa tattalin arziki, da kuma kara azama kan samar da kayayyaki masu inganci. (Tasallah)