A wannan rana da yamma, Li Keqiang ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu da ke ziyara a Beijing, sun kuma halarci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyoyin yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 ta fuskar aikin gona, kimiyya da fasaha, harkokin ilmi da dai sauransu.
A cikin shawarwarin, Li Keqiang ya nuna cewa, batun Palasdinu, muhimmin batu ne da ke shafar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya. Warware batun cikin lumana ta hanyar yin shawarwari da tattaunawa, ita ce hanya daya tilo, hakan ya dace da moriyar Isra'ila da Palasdinu, haka kuma yana amfanawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da ma duniya baki daya. Kasar Sin tana son yin kokari tare da bangarori masu ruwa da tsaki wajen wanzar da zaman lafiya a yankin na Gabas ta Tsakiya cikin himma da kwazo.
Har wa yau Li Keqiang ya ce, yin hadin gwiwar a-zo-a-gani, wani bangare ne na huldar da ke tsakanin Sin da Isra'ila, wanda ya fi samun saurin bunkasuwa da kwazo, yana kuma da makoma mafi haske. Wajibi ne kasashen 2 su yi kokarin kyautata hadin gwiwarsu a sassa daban daban, a kokarin kara kawo wa jama'ar su alheri.
A nasa bangaren kuma, Benjamin Netanyahu ya ce, Isra'ila ta girmama nasarorin da kasar Sin ta samu ta fuskar bunkasuwa, tana son yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen kara raya huldar da ke tsakaninsu bisa fifikon da suke da shi. Kana kuma Isra'ila ta yaba wa rawar da kasar Sin ta taka a fannin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.(Tasallah)