in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Jacob Zuma a Najeriya
2013-04-17 10:51:26 cri

Bisa goron gayyatar da aka bashi, shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya yi wata ziyarar aiki ta yini daya a kasar Najeriya a ranar talata 16 ga watannan. Ga rahoto da wakilinmu Murtala ya hada mana daga fadar gwamnatin Najeriyar dake birnin Abuja, wato "Aso rock villa".

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya zo nan fadar shugaban kasa dake Abuja ne da misalin karfe 1 na yamma, inda takwaransa na kasar Najeriya Dr. Goodluck Jonathan ya shirya wani gagarumin biki don maraba da zuwanshi Najeriyar.

A matsayinsa na shugaban kasar Afirka ta Kudu, wadda ta kasance kasa mai arziki sosai a Afirka, ziyarar Jacob Zuma a wannan karo ta janyo hankalin kafafen watsa labarai da dama.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China