Ofishin kula da 'yan gudun hijira na MDD ya ce, a kalla mutane 55 ne suka nutse, wasu kuma suka bace bayan da jirgin ruwan dake dauke da su ya kife a gabar tekun Somaliya, sakamakon cunkuson da ya yi a daren ranar Talata, abin da ya zama hadari mafi girma a gaban tekun Aden a cikin shekaru biyu da suka gabata, inji kakakin ofishin Eduardo Del Buey.
A lokacin da yake ma manema labaran karin bayani Del Buey ya ce, wannan ne hadari mafi girma wanda ya jawo asaran rayuka a gabar Aden tun watan Fabrairun shekarar 2011, a cewarsa, mutane biyar da suka tsira da rayukansu sun yi bayanin cewa, jirgin dake makare da mutanen ya samu matsala ne jim kadan da barin tashar Bosasso na arewacin Somaliya, kuma ya kifar da daukacin mutane 60 dake cikinsa mintuna 15 da fara tafiyarsa a kan ruwa, wadanda galibinsu 'yan kasashen Somaliya ne da Habasha cikin teku.
Del Buey ya yi bayanin cewa, ya zuwa lokacin da yake magana da manema labarai, an gano gawawwaki 23 da suka hada da mata 14, maza 8 da wani 'dan karamin yaro da bai wuce shekaru 4 ba shi kadai, sauran 32 kuma ana kyautata zaton sun nutse.
Mutane 100,000 ne suka tsallaka bahar Malia da gabar tekun Aden wannan shekarar, duk da gargadin da ofishin kula da 'yan gudun hijira na MDD suka yi na hadarin dake cikin irin wannan tafiya.
Ya ce, abin damuwa shi ne jiragen ruwan da ake amfani da su sun tsufa, don haka ba su cancanta ba, sannan ana daukan mutane fiye da karfin jirgin, bugu da kari, mutanen sun bar yankin na kahon Afrika don neman wani wurin da za su samu ingancin rayuwa, su kan fada hannun 'yan fasa kwarin mutane, su kan fuskanci munanan abubuwa, har da rasa rayukansu.(Fatimah)