in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar ANC ta kasar Afrika ta kudu za ta shugabanci jama'ar kasar ga yin sabbin sauye-sauye
2012-12-21 16:43:18 cri

Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya sanar a ran 20 ga wata a birnin Cape Town cewa, jam'iyyar ANC ta kasar Afrika ta kudu, a matsayinta na daya daga cikin jam'iyyu uku dake jan ragamar mulkin kasar cikin hadin gwiwa za ta yi iyakacin kokarinta wajen jagorantar jama'ar kasar domin yin sabbin sauye-sauye.

A gun bikin rufe babban taron wakilai karo na 53 da jam'iyyar ANC ta yi, Jacob Zuma ya yi kira ga mambobin jam'iyyar da su kara hadin gwiwa tare da kawar da bambancin ra'ayi, ta yadda za su kara kawo wa jam'yyar inganci.

Ya ce, yanzu kasar ta shiga wani muhimmin lokaci na yin gyare-gyare karo na biyu bayan an kawo karshen manufar wariyar launin fata, Sabo da haka, ana bukatar wata jam'iyya mai karfi, tare da jadadda cewa jam'iyyar ANC za ta dauki nauyin aikin da tarihi ya danka mata.

An kawo karshen babban taron ANC karo na 53 a ran 18 ga wata a birnin Bloemfontein cibiyar doka ta kasar, inda wakilai kimanin 4500 da suka zo daga larduna 9 sun halarci taron.

A gun taron, shugaban jam'iyyar Jacob Zuma ya doke abokin hamayyarsa wato mataimakin shugaban kasar Kgalema Motlanthe inda sakamakon wannan nasara zai ci gaba kan mukaminsa na shugaban jam'iyyar ANC. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China