Yayin da yake gabatar da rahoton siyasa a wajen bikin bude taron, shugaban jam'iyyar ANC na yanzu, kuma shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, jam'iyyarsa da sauran jam'iyyun siyasar kasar suna kokarin yin aiki kafada da kafada, inda hakan ya taimakawa kasar Afirka ta Kudu wajen samun ci gaba a fannoni da dama kamar na siyasa, tattalin arziki, diflomasiyya, al'adu da dai sauransu.
Ya ci gaba da cewa jam'iyyar ANC za ta ci gaba da jagorantar al'ummar kasar don raya tattalin arziki da masana'antu, da kuma kara samar da guraban ayyukan yi, tare da zummar kyautata zaman rayuwar al'umma.
An ce, a yayin wannan taro ne za'a zabi sabbin shugabannin jam'iyyar ANC, ciki har da sabon shugabanta.
Jam'iyyar ANC, jam'iyya ce mai mulki kuma mafi girma a kasar Afirka ta Kudu, kuma mai yiwuwa sabon shugabanta zai lashe zaben shugaban kasar a shekara ta 2014.(Murtala)