in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yankewa wasu mahara su biyu hukuncin kisa, bisa kisan mutane 500 da suka yi a Algeria
2013-05-06 10:34:48 cri

Wata kotun hukunta manyan laifuka a kasar Algeria, ta zartas da hukuncin kisa ga wasu mahara biyu, wadanda ta samu da laifin kashe wasu mutane 500, tare da cin zarafin wasu mata kimanin 60.

Kamfanin dillancin labarai na APS ya rawaito cewa, kotun ta yankewa Kouri Djillali, da Antar Ali hukuncin kisan ne, bayan sun amince da shiga wata kungiyar 'yan ta'adda dake lardin Chlef a shekarar 1997, yankin da ke da tazarar kilomita 200 daga gabashin birnin Algiers, sun kuma ce karkashin wannan kungiya sun hallaka sojoji, da fararen hula da dama a lardunan Boumerdes, da Medea, da Tiaret, da Chlef, da Relizane da kuma Blida.

Har ila yau, masu laifin sun amince da aikata laifin cin zarafin mata masu yawa a wadannan wurare a shekarar 1999.

Kasar Algeria dai ta fada rikice-rikice ne cikin shekarun 1990, ko da yake a baya-bayan nan, yanayin tsaron kasar ya fara kyautatuwa, bayan da mahukuntan kasar suka amince da aiwatar da manufar sulhu, da kuma tsaurara matakan tsaro a fadin kasar. Sai dai duk da wadannan matakai da ake dauka, 'yan ta'adda na ci gaba da kai hare-hare kan sojoji da 'yan sanda a arewa maso gabashi, da kuma kudancin yankunan kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China