in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban jam'iyyar dake mulki a kasar Algeriya ya ajiye aiki
2013-01-04 10:01:40 cri

Shugaban jam'iyyar dake kan mulki a kasar Algeriya RND Ahmed Ouyahia ya sanar da ajiye aikinsa a matsayin babban magatakardar jam'iyyar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar APS ta ba da labari a jiya Alhamis 3 ga wata.

Mai magana da yawun jam'iyyar Miloud Chorfi ya yi bayanin cewa, da kansa Mr. Ouyahia ya aika da wasika wanda a ciki ya ayyana bukatarsa na ajiye aikin a matsayin shugaban jam'iyyar, sai dai kuma zai cigaba da ayyukansa na gwagwarmayyar neman 'yancin talakawa a jam'iyyar, don haka yanzu za'a sanar da ajiye aikin a hukumance lokacin babban taron jam'iyyar a ranar 15 ga watan nan.

Jam'iyyar RND ta dade tana rawa na 'yan watannin sakamakon wani bangarenta dake goyon bayan tsohon ministan kiwon lafiya da motsa jiki na kasar Yahia Guidoum wadanda ke ta ikirarin tun ba yau ba cewa, Ahmed Ouyahia ya ajiye aiki.

Bayan ajiye aikin manyan shugabannin jam'iyyun adawa biyu, RCD da FFS, yanzu shi ne na RND shi ma ya bi sahun wanda a bayan shi ana sa ran na FLN wanda ita ma tana da kaso a mulkin kasar, kuma daman ana ta takaran mukamin wanda Abdelaziz Belkhadem ke jagoranta.

RND da FFS su ne manyan jam'iyyu biyu masu mulki a Algeria saboda suna da adadi daya a majalisar dokoki da kuma zartaswa.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China