in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin ruwa na kasar Sin sun kai ziyara a kasar Aljeriya
2013-04-03 09:58:39 cri

Rundunar sojojin ruwa ta kasar Sin mai aikin rakiya, rukuni na goma sha uku ya isa Algiers, babban birnin kasar Aljeriya rana Talata don ziyarar kwanaki hudu a kasar.

Wannan ziyara ta rundunar sojin ruwan masu rakiya, da ta kunshi manyan jiragen ruwan soja guda biyu da jirgin daukar kayayyakin bukata guda daya, ita ce ta farko da rundunar sojojin ruwan kasar Sin ta kai kasar, in ji kwamandan rukunin, Li Xiaoyan.

A yayin ziyarar, Rear Admiral Li zai gana da kwamandan sojojin ruwa na kasar Aljeriya Malek Necib da ma sauran manyan jami'an sojojin ruwa na kasar, kana zai bayyana ayyukan da sojojin ruwa na kasar Sin ke yi dangane da yaki da 'yan fashin teku a kan tekun Aden da na Somaliya.

Ya zuwa yanzu dai, rundunar sojin ruwan rukuni na goma sha uku, ta yi aikin rakiya a teku a madadin kasar Sin na tsawon watanni hudu a tekun Aden da na Somaliya kafin ya bar yankin a ran 18 ga watan Maris don aikin kai ziyara a kasashe.

Kasar Aljeriya ita ce kasa ta biyu da rundunar ta kai ziyara, wato bayan ziyara da ta kai a kasar Malta tsakanin 26 zuwa 30 ga watan Maris, inda kuma daga bisani za ta kai ziyara kasashen Morocco, Portugal da Faransa.

Jiragen ruwan yaki na sojojin kasar Sin na aikin yaki da 'yan fashin teku a wuraren tekun Somaliya tun cikin watan Disamban shekarar 2008. Zuwa yanzu dai rundunar sojojin ruwa ta kasar Sin ta cimma nasarar yiwa jiragen 'yan kasuwa sama da dubu biyar rakiya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China