Wata kotu a kasar Aljeriya a ranar Talata ta yanke hukuncin kisa kan wani babban jami'in kungiyar dake da alaka da kungiyar Al-Qaida, tare da wasu 'yan ta'adda biyar duk da cewa ba su kasance a kotun ba, in ji kamfanin dillancin labaran kasar, APS.
Kotun tuhumar masu manyan laifuffuka dake Algiers ta tuhumi Mokhtar Belmokhtar da ake wa lakabi da Al-Aouer wato mai ido daya, da kasancewa cikin kungiyar 'yan ta'adda da kuma yi wa harkar tsaro a kasar zagon kasa.
Belmokhtar da wasu 'yan ta'adda guda biyar har wa yau an tuhume su da shirya da kuma gudanar da harin ta'addanci a masana'antar iskar gas ta Tiguentourine dake kudu maso gabashin kasar Aljeriya.
Ana kyautata zaton cewa, Belmokhtar shi ne ya shirya garkuwa da mutane da aka yi a masana'antar gas ta Tiguentourine a cikin watan Janairun 2013, inda hakan ya yi sanadin mutuwar 'yan kasar waje guda 38.
Rahotanni na nuna cewa, an kashe Belmokhtar da wani babban jami'in kungiyar Al-Qaida a yankin Maghreb (AQIM), Ahmed Ghedir wanda ake wa lakabi da Abu Zeid, a arewacin kasar Mali yayin wani sumame da dakarun kasar Chadi wadanda ke aiki da rundunar sojin Afirka karkashin jagorancin dakarun Faransa, suka yi a Mali cikin watan Maris.(Lami)