in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka wasu 'yan tawaye 3 a kusa da kan iyakar Algeria
2013-01-15 14:21:06 cri

Sojojin gwamnatin kasar Algeria sun harbe wasu 'yan tawaye 3 a yankin dake kan iyakar kasar ta kudu, dake makwabtaka da kasashen Niger da Libya. Ma'aikatar tsaron kasar ta Algeria ce dai ta tabbatar da faruwar wannan lamari ga kamfanin dillacin labaran kasar APS, tana mai cewa, an kai wannan hari kan maharan ne ranar Litinin 14 ga wata, a yankunan saharar Meskeline dake daura da Djanet mai nisan kilomita 2,180 daga kudu maso gabashin birnin Algiers. An ce, 'yan tawayen na kokarin kutsawa cikin kasar ta Algeria ne ta wannan yanki yayin da sojojin suka far musu, ko da yake dai ba a bayyana ko daga wace kasar suke ba. Bugu da kari, rundunar sojojin ta ce, ta samu nasarar kwace wata mota da wasu makamai daga hannun maharan.

Kasar Algeria dai na ci gaba da daukar matakan kare kan iyakokinta, don gudun kwararar 'yan tawaye, musamman ma daga Mali, wadanda a yanzu haka ke dauki-ba-dadi da sojojin kasar, dake samun tallafi daga sojojin saman kasar Faransa a yankunan arewacin kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China