in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Statoil na Norway ya bayyana niyyarsa na sake tafiyar da harkokinsa a Aljeriya
2013-03-01 11:09:29 cri

Kamfanin makamashin kasar Norway Statoil da ya dakatar da ayyukansa a kasar Aljeriya tun bayan wani harin da aka kai a cikin watan Janairun da ya gabata a wata tashar harkar gas ta Tigentourine ya bayyana niyyarsa na sake fara ayyukansa, a cewar babban darektan wannan kamfani mista Helge Lund a ranar Alhamis a yayin wata ganawa tare da ministan makamashi da ma'adinai na kasar Aljeriya, mista Yousef Yousti, a wani labari da kamfanin dillancin labarai na APS ya rawaito.

Kamfanin hakar gas na In Amenas, dake gundumar Illizi mai tazarar kilomita 1700 a kudu maso gabashin birnin Alger na karkashin hannun kamfanin Sonatrach na kasar Aljeriya, kamfanin BP na kasar Ingila da kuma kamfanin Statoil na Norway ya sake fara gudanar da ayyukansa a ranar 24 ga watan Febrairu.

A ranar 16 ga watan Janairun da ya gabata ne wani gungun 'yan ta'adda ya kai hari kan tashar hakar gas ta Tiguentourine tare da yin garkuwa da ma'aikatan wurin kimanin 800. Kwashe gari, rundunar sojojin kasar Aljeriya ta kai wani samame domin kwato ma'aikatan da aka yi garkuwa da su, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 37, wanda a cikinsu akwai darektan kamfanin Statoil reshen kasar Aljeriya, Victor Sneberg. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China