Kungiyar kasashen yankin Maghreb na Larabawa (UMA) ta bayyana cewa, ya kamata a daidaita rikicin kasar Mali daga dukkan fannoni, sannan kuma ba a tsaya a bangaren soja kawai ba, in ji ministan harkokin wajen kasar Libya, Mohamed Abdelaziz a ranar Lahadi a birnin Rabat.
Duk wata tawagar MDD a kasar Mali, ba za ta tsaya kan aikin gargajiya na wanzar da zaman lafiya ba, amma ya kamata ta yi aiki bisa hangen da zai shafi dukkan fannoni domin warware wannan rikici, tare da hadin gwiwar kungiyar ECOWAS, in ji mista Abdelaziz a yayin wani taron menama labarai bayan wani taron kwamitin ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar UMA.
Jami'in diplomasiyyar kasar Libya ya jaddada cewa, ana bukatar tawagar MDD da ta ba da taimako wajen sake gina kasar Mali da taimaka wa shirya mulkin wucin gadi na demokaradiya yadda ya kamata ta hanyar gudanar da zabubuka cikin 'yanci da adalci da kuma sabunta hukumomin kasar. Haka shi ma takwaransa na kasar Mauritaniya, Hamid Ould Hamid ya bayyana cewa, taron karo na 31 ya cimma matsaya mai kyau game da daidaita rikicin kasar Mali, ta yadda za'a iyar kiyaye tsaron wannan kasa.
Kwamitin sulhu na MDD ya ba da amincewarsa a ranar 25 ga watan Afrilun da ya gabata kan kafa wata rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar Mali. Kimanin sojojin MDD 12600 ne suna zaman nauyin kawo zaman lafiya a arewacin kasar Mali, a cikin tawagar MDD ta MISNUSMA wadda za ta maye gurbin sojojin kasashen Afrika na MISMA. (Maman Ada)