in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya amince da tura tawagar samar da zaman lafiya a Mali
2013-04-26 12:32:17 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya dauki mataki a ranar Alhamis na kafa tawagar kasa da kasa ta MDD domin maido da zaman lafiya a kasar Mali (MINUSMA) dake kunshe da sojoji da 'yan sanda 12600, wadanda za su maye gurbin tawagar kasa da kasa kan tallafawa kasar Mali dake karkashin jagorancin Afrika (MISMA) daga bakin ranar daya ga watan Yulin shekarar 2013 domin samar da zaman lafiya da tsaro a kasar Mali ta kowane hali.

Mun san halin da ake ciki ba shi da daidaituwa ba, in ji mataimakin sakatare janar na MDD kan ayyukan samar da zaman lafiya, Herve Ladsous yayin da yake shedawa 'yan jarida a gaban kwamitin sulhu, bayan kafa tawagar MINUSMA.

Nauyin aikin wannan tawaga zai hada da ayyukan MISMA na yanzu da kuma na cibiyar MDD a kasar Mali (BUNUMA), domin kawo sauki kan tuntubar juna tsakanin gwamnatin kasar Mali da gungun jam'iyyun adawa dake fatan halarta wajen cimma wata masalaha ta siyasa domin ganin an shirya zabubukan shugaban kasa da na 'yan majalisa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China