Mataimakin babban darekta na kungiyar 'ONG Plan International' mai zaman kanta, dake ziyarar aiki a kasar Mali, ya yi kira a ranar Asabar a birnin Bamako wajen ganin an tattara dalar Amurka miliyan 9 da dubu 600 domin taimakawa yaran da yaki ya rutsa da su a kasar Mali.
Mataimakin babban darektan 'ONG Plan International', Tjipke Bergsma da ya kai rangadi a yankunan Segou a tsakiyar kasar da kuma birnin Toumbouctou ya bayyana cewa, bisa 'yan Mali dubu 450 da suka yi gudun hijira ko suka kaura, kashi 51 cikin 100 kananan yara ne wadanda ba su samu damar zuwa makaranta ba dalilin mamayen 'yan kishin Islama, amma ana kokarin tabbatar da dawowar zaman lafiya, shi ya sa, wannan matsala ta fara kyautatuwa.
Mista Kjipke Bergsma ya yi kira ga gwamnatocin kasashe da kungiyoyi masu ba da tallafi da kada su manta da yara a cikin kasafin kudadensu na tsaron kasar Mali, a ganinsa kuma ya kamata wadannan gwamntoci da kungiyoyi dake ba da tallafi su kebe wani kaso daga cikin kasafin kudin yaki ga bukatun ayyukan jin kai ga yara wadannan yake-yake suka rutsa da su.
Haka kuma ya bayyana cewa, kungiyarsa ta amince kara ayyukanta bisa karin Sefa miliyan 500 tun farko barkewar wannan rikici.
A karshe, mista Bergsma ya bayyana cewa, kungiyarsa ta yi wannan kira na neman dalar Amurka miliyan 9 da dubu 600 domin taimakawa yaran Mali komawa makaranta, samar da tsabtattun ruwan sha, ba da kulawa ta fuskar kiwon lafiya da dai sauransu. (Maman Ada)