in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Hollande ya gana da Annan dangane da batun kasar Mali
2013-05-03 09:41:15 cri

A ranar Alhamis, shugaban kasar Faransa, Francoise Hollande ya yi maraba da zuwan tsohon sakatare janar na MDD Kofi Annan a fadar Elysee, don tattaunawa dangane da yanayin da ake ciki a kasar Mali da kuma ayyukan kafa zaman lafiya da MDD ke yi a kasar ta yammacin Afirka.

A yayin ganawar, shugaban ya tabo batun taron kasa da kasa dangane da halin da ake ciki a Mali, wanda kuma shi ne zai zamo shugaban taro na biyu, tare da shugaban rikon kwarya na kasar Mali da kuma shugaban hukumar gudanar da kungiyar tarayyar Turai, wanda aka shirya gabatarwa ran 15 ga watan Mayu a Brussels, in ji wata sanarwar da ta fito daga ofishin shugaba Hollande.

Haka zalika, shugaba Hollande da Annan sun kuma yi musayar ra'ayi dangane da batun yaki da safarar miyagun kwayoyi, wanda ke barazana ga tsaro da dorewar yankin yammacin Afirka.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China