Gidan rediyon RFM mai zaman kansa, ya ba da rahoton fara daukar sojojin, to amma bai ba da cikakken bayani kan tsarin kawo sojojin na Senegal ba.
A ranar Laraban makon da ya wuce ne shugaban kasar Senegal Macky Sall, ta wani sako da ya tura majalisar dokokin kasar, ya bukaci 'yan kasar su hada kai su kuma nuna goyon baya ga aikin tura sojojin Senegal guda 500 zuwa kasar Mali.
A fadar shugaban kasar, duk wani abu da ya shafi kasar Mali zai zamo abin damuwa ga kasar Senegal.
Bisa kudurin majalisar tsaro ta MDD, kungiyar ECOWAS ta kuduri hada sojoji 3,300 don su taimakawa gwamnatin kasar Mali ta yaki 'yan tawaye dake rike da rabin yankin arewacin kasar tun watan Maris na shekarar 2012 sakamakon wani juyin mulki na soja.
Kungiyar 'yan tawayen da ake ganin tana da goyon baya daga kungiyar Al-Qaida, an dauke ta a matsayin babbar barazana ga tsaro a yankin da kuma ga gwamnatin kasar Mali.
Tun cikin makon da ya wuce dakarun kasar Faransa ke wa 'yan tawayen luguden wuta inda suka taimaki sojojin gwamnatin Mali wajen kwato garuruwa guda biyu wadanda 'yan tawayen suka yi nasarar karbarsu a yaki. (Lami Ali)