in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a soke majalisar dattijai da mukamin mataimakin shugaban kasa a Senegal
2012-09-20 14:29:36 cri
A ran 19 ga watan, a kasar Senegal, an zartas da dokar soke majalisar dattijai da mukamin mataimakin shugaban kasar ta hanyar kada kuri'a bayan babban taron hadaddiyar majalisar dokokin kasar da majalisar dattijai.

An zartas da dokar bisa yawan kuri'u 176 wanda ya bada kashi uku cikin biyar na 'yan majalisar, hakan ya dace da tanadin dokar da abin ya shafa ta kasar. Duk da haka, wasu 'yan majalisar dokoki da ta dattijai sun nuna kiyayya ga aikin.

Majalisar dattijan kasar Senegal tana kunshe da mambobi 100, kuma tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade ya nada yawancinsu, ban da wannan kuma, Abdoulaye Wade ya kafa mukamin mataimakin shugaban kasar, amma ba wanda ya taba hau kan wannan kujera.

A karshen watan Agustan da ya gabata, shugaban Senegal Macky Sall ya gabatar da wani shirin soke majalisar dattijai bisa dalilin rage yawan kudin da gwamnatin kasar take kashewa domin ba da agaji ga masu fama da bala'in ruwa a kasar ga majalisar dokokin jama'ar kasar cikin gaggawa, inda ya nuna cewa, majalisar dattijan kasar ta kashe kudi da yawa, amma ba ta taimaka ko kadan ba, shi ya sa, za a yi amfani da kasafin kudinta da yawansa ya kai kusan Sefa biliyan 8 wato kimanin dalar Amurka miliyan 16 kan aikin shawo kan bala'in ruwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China