A cikin sabuwar majalisar ministoci, gwamnatin Mahama ta kara kago wata sabuwar ma'aikatar kula da harkokin kamun kifaye da amfanin ruwa, kuma ta canja ma'aikatar makamashi zuwa ma'aikatar kula da makamashi da iskar gas, haka kuma a cikin sabuwar majalisar ministoci, babu wani minista da aka sake nada shi kan mukaminsa.
Ban da wannan kuma, shugaba Mahama shi ma ya nada ministan fadar shugaban kasar da karamin minista, da sauran manyan jami'an hukumomin kasar, kuma nan ba da jimawa ba majalisar dokokin kasar za ta ba da amincewarta kan wannan sabuwar gwamnatin kasar.(Bako)