Wasu bayanai da kamfanin dillancin labarai na kasar Ghana ya fitar, sun bayyana cewa shugaban kasar John Dramani Mahama ya yi wata ganawar sirri da shugaban rundunar tsaron kasar Birtaniya Sir David Richards, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi rikicin kasar Mali.
Yayin taron wanda ya gudana a birnin Accra na kasar ta Ghana ranar Asabar 2 ga wata, a cewar kakakin rundunar sojin Ghana Kanar Nbawine Atintande, Sir Richards ya alkawarta baiwa Ghanan jirgin sama da zai yi jigilar dakarunta kimanin 120, wadanda mafi yawansu injiniyoyi ne zuwa Mali.
Richard ya kara da cewa, dangantaka tsakanin kasashen biyu na da dadadden tarihi, kuma ya yi fatan ziyarar tasa ta wannan lokaci za ta kara bunkasa ta.
Atintande ya ce Ghana za ta dukufa wajen karfafa alakarta da ragowar takwarorinta, domin cimma buri kan ci gaba da ta sa a gaba.(Saminu)