in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana na burin noma shinkafa ton miliyan 1.2 cikin shekaru 5
2013-01-24 09:26:55 cri
Wani jigo a masana'antar noma a kasar Ghana ya yi bayani ranar Laraba cewa kasar na burin noma ton miliyan 1.2 na shinkafa nan da shekaru 5 masu zuwa don rage dogaro da kasar ke yi kan shinkafa da ake kawowa daga kasashen waje.

Babban Sakataren kungiyar kwararru masu harkar shinkafa a kasar Ghana, (GRIB) Paa Kwesi Forson shi ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua inda ya ce idan aka samu samar da horo ga karin manoma a kasar wadanda za su iya noma shinkafa da yawanta ya kai ton shida wato daidai da metric ton 1.2 ke nan, ko shakka babu za'a kawar da harkar shigowa da shinkafa daga waje.

Kungiyar ta GRIB ta bayyana cewa kasar ta samu ci gaba matuka, amma sannu a hankali, a fannin noman amfanin gona dangin shinkafa, inda yawan wanda ake nomawa ya karu daga ton 249,999 a shekarar 2006 zuwa ton 491,603 a shekarar 2010.

Yanzu haka kasar na samar da shinkafa da take bukata da ya kai kashi 45 daga cikin dari wato ke nan sauran kashi 55.

Saboda hakan ne ake kira ga gwamnatin kasar Ghana da ta zabga kudin haraji kan shinkafa da ake kawowa daga waje domin a samu karfin gwiwar zuba jari a noman shinkafa a cikin gida.

A halin yanzu masu ruwa da tsaki a wannan harka na kokarin shawo kan dukkan wasu kalubale, domin kasar Ghana ta zamo mai dogaro da kai a fannin noman shinkafa.

Shinkafa itace ke biye da masara cikin abinci mafiya daraja a kasar ta Ghana kuma ana samun karin cin shinkafar saboda karuwar yawan jama'a, habakar birane da kuma halayen jama'a.

Shinkafa na samar da kashi 9 cikin dari na bukatun abinci a kasar kana manufar bunkasa harkokin samar da abinci da noma na Ghana (FASDEP) ta bayyana shinkafa a matsayin abinci dake da muhimmanci wanda kuma ke bukatar mai da hankali na musamman don a cimma burin samar da abinci. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China