Shugaban majalisar, David Mark ya yi wannan kira a ranar Asabar, tare da jaddada cewa babu wata gwamnati da za ta rike hannu tana kallon al'ummarta da bata ci bata sha ba ana kashe su ko ana raunata su a cikin makarantu, kasuwanni, mujami'o'i da masallatai.
" ina son yin kira musammun ma ga mambobin Boko Haram, wakilansu, masu ba su taimako da kuma masu nuna masu goyon baya da su yi kokarin shiga shawarwari da suka zama wajibi yanzu", in ji mista Mark tare yin alkawarin cewa majalisarsa za ta taimakawa gwamnati wajen daidaita wannan matsala ta ta'adanci. (Maman Ada)