A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, Lagarde ta bayyana cewa, sabo da kasashe masu wadata kamar na Turai da Amurka sun dauki kwararan matakai wajen hada-hadar kudia shekarar da ta wuce, abin ya karfafa zukatan jama'a, amma kasashe masu wadata na fuskantar wani kalubale, wato rashin aiwatar da manufa cikin dogon lokaci, musamman ma wajen tsara wani shirin rage yawan bashi cikin matsakaici da dogon lokaci.
Lagarde ta ci gaba da bayyana cewa, an kiyasta cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da habaka da sauri, daga raguwar yawan rarar kudin da ta samu wajen cinikin kasashen waje, ana iya gane cewa Sin na daidaita tsarin tattalin arziki ta fuskar kara yawan bukatun ciniki.(Bako)