in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hasashen da asusun IMF ya yi kan karuwar tattalin arzikin duniya a shekarar 2013 da ta 2014 ya ragu
2013-01-24 14:15:26 cri
Ran 23 ga wata, asusun ba da lamuni na duniya IMF wanda hedkwatarsa ke birnin Washington ya rage adadin karuwar tattalin arzikin duniya na shekarar 2013 da ta 2014 zuwa kashi 3.5 bisa dari da kuma kashi 4.1 bisa dari.

Wadannan adadin sun ragu da kashi 0.1 bisa dari idan an kwatanta da adadin da asusun ya yi a watan Oktoba na shekarar 2012. Bugu da kari, asusun ya yi gargadi cewar, akwai kalubale da dama da ake fuskanta wajen farfado da tattalin arzikin duniya.

Bisa hasashen da aka yi, an ce, tattalin arzikin yanki da ke amfani da kudin Euro zai ragu da kashi 0.2 bisa dari a shekarar bana, kana zai karu da kashi 1.0 bisa dari a shekara mai zuwa.

Tattalin arzikin kasar Sin zai karu da kashi 8.2 bisa dari da kuma kashi 8.5 bisa dari daki daki, a shekarar bana da kuma shekara mai zuwa, kuma adadin ya yi daidai da hasashen da asusun ya bayar a wancan gami.

Asusun ba da lamuni na IMF ya nuna cewa, a halin yanzu ana fuskantar kalubale da dama wajen farfado da tattalin arzikin duniya, sabo da ba a iya tabbatar da karuwar tattalin arziki na yankin da ke yin amfani da kudin Euro a nan gaba, kuma watakila nan gaba kadan, Amurka za ta dauki matakan tsuke bakin aljihun gwamnatinta.

Don haka ake ganin cewa ya kamata, hukumomin da abin ya shafa su dauki matakan da za su dace wajen warware matsalolin da za a fuskanta cikin sauri. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China